Ainihin wadanda suka shirya zanga zanga a Sudan, sun yi kira da a mika mulki nan da nan ga gwamnatin farar hula, bayan da sojoji su ka yi juyin mulki wanda ya kai ga hambarar da shugaba Omar Al-Bashi a satin da ya gabata.
A jiya Lahadi, majalisar mulkin soja din ta ce za ta bayyana Firaiminsta farar hula da kuma majalisar ministoci su taimaka wajen shugabancin kasar, amma ba za su nada farar hula a matsayin shugaban kasa ba.
Mai Magana da yawun sojojin ya kuma ce majalisar ba za ta hana yin zanga zangar da ake ci gaba da yi ba. Za a ci gaba da gani ko sanarwar za ta gamsar da masu zanga zangar, wadanda su ka bukaci majalisar “batare da bata lokaci ba, kuma ba tare da wani sharadi ba” ta mika mulki ga farar hula.
Kungiyar kwararru a fannoni daban-daban na mutanen Sudan, wacce ta jagoranci zanga zangar, ta yi kiran da kafa gwamantin farar hula, tare da kiran a ci gaba da gudanar da zanga zanga har sai an biya musu bukatarsu.
Facebook Forum