WASHINGTON, DC —
Litinin dinnan, masu zanga zanga, wadanda ke goyon bayan kasar Rasha suka yi kunnen kashi ga wa'adin da gwamnatin Ukraine ta basu na janyewa daga gine ginen da suka mamaye, domin ayi musu ahuwa, a yayinda shugaban rikon kwaryar Ukraine yayi barazanar cewa zaiyi amfani da karfin soja domin fatattakar su.
Masu zanga zanga da dama ne suka fasa tagogi a hedikwatar yan sanda a birnin Horlivka dake gabashin kasar suka yi dambe da yan sanda a lokacinda suka mamaye ginin.
Shugaba Barack Obama na Amirka ya yiwa takwaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin kashedi ta wayan tarho jiya Litinin cewa, idan al'amarin na Ukraine ya ci gaba da kamari, Rasha za'a dorawa alhaki.
Haka kuma shugaba Obama yayi kira ga shugaban na Rasha da yayi amfani da tasirinsa wajen shawo kan masu zanga zanga su janye ko kuma su fice daga gine ginen da suka mamaye.
Shi kuma a nashi bangaren, shugaba Putin ya bukaci Mr Obama da yayi kokarin hana gwamnatin Ukraine amfani da karfin soja akan masu zanga zanga.