A watan Disamban bara ne wakilan kungiyoyin manoman albasa dake Nijar a karkashin shugabancin shugaban kasar, Mahammadou Issoufou, suka gana da wasu masu hannu da shuni a kasar Faransa domin neman hanyar habaka noma da sarafa albasa a kasar.
A lokacin ganawar ce masu hannu da shuni suka yi alkawarin dafawa manoman da girka injin na nika albasa cikin kasar ta Nijar.
Yanzu dai masu hannu da shunin sun isa garin Madawa a jihar Toua, garin da ya kasance inda aka fi noman albasa a duk fadin kasar. Injiniya Blaise Madunga shi ne wakilin kungiyar da ta sha alwashin tallafawa manoma albasa a kasar ta Nijar ta hanyar nika albasa da romaji.
Bisa bayanin da Blaise Madunga ya yi sun gana da masu hannu da shuni na cikin kasar da su ma zasu ba da nasu tallafin a matsayin saka jari.
Inji Madunga sun ziyarci gonakan manoman, sun yi taro da kungiyoyinsu kuma sun himmatu.
A taron masu hannu da shuni da manoman albasa, Malam Bubakar Adamu daraktan zauren 'yan kasuwa, manoma da masu aikin hannu ya ce daya daga cikin matsalolin dake hana ruwa gudu a harkokin manoma albasa a Nijar shi ne daukar takardar da duk wanda zai fita da albasa daga kasar sai ya riketa.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.
Facebook Forum