Dubban mutane ne aka kiyasta cewa sun tsere daga mazauninsu don zuwa neman mafaka daga lokacin da kungiyoyin ta’addanci suka fara kawo farmaki a Nijar daga shekarar 2015 kawo yau, abin da ke tayar da hankalin kungiyoyin kare muradan jama’a irinsu gamayyar CCAC kamar yadda Nouhou Mahamadou Arzika ya bayyana a sanarwar da suka fitar.
Lura da yadda wannan al’amari ke da nasaba da abin da suka kira halin ko in kula ko kuma rikon sakainar kashin da wasu manyan jami’an gwamnati ke yi wa maganar tsaro, ya sa kungiyoyin suka kudiri aniyar gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi 15 ga watan Maris a daukacin manyan biranen Nijar.
To sai dai ra’ayoyi sun sha bamban akan wannan batu. Masu kare manufofin gwamnatin irinsu shugaban kungiyar NCC Gyara Kayanka, Mohamed Abdoulkader, na ganin abin bai kai a matsa wa hukumomi lamba ba ya kuma ce kamata yayi a bari a ga irin binciken da gwamnati zata yi.
Kungiyoyin kwadago da kungiyar dalibai ta kasa, da kungiyoyin malaman jami’o’i da makarantun firamare da na sakandare, da kuma wasu kungiyoyin direbobi sun bada sanarwar goyon bayan kungiyoyin fafutika na CCAC, a saboda haka suka umurci daukacin magoya bayansu su hallara a wurin wannan taron gangamin neman haske akan yadda ake tafiyar da sha’anin tsaro a Nijar.
Ga cikakken rahoton cikin sauti.