Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Coronavirus Na Karuwa a Najeriya


Wasu jami'an lafiya suna gwaje-gwajen cutar coronavirus a kasar Morocco
Wasu jami'an lafiya suna gwaje-gwajen cutar coronavirus a kasar Morocco

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa adadin mutanen da ke dauke da COVID-19, wacce ke haddasa cutar coronavirus na karuwa.

Hukumar kare yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta ce a ranar Asabar an samu karin mutum 49 da ke dauke da cutar.

“Ya zuwa karfe 10:40 na dare na ranar 18 ga watan Afrilu, an tabbatar mutum 542 na dauke da #COVID19 a Najeriya,” a cewar shafin Twitter hukumar ta NCDC.

Hukumar ta kara da cewa, mutum 19 ne suka mutu ya zuwa yanzu kana an sallami 166.

A halin da ake ciki jihar Legas ce aka fi samun masu dauke da cutar wadanda adadinsu ya kai 306.

Sai babban birnin kasar Abuja mai mutum 81, sai kuma Kano da ke da mutum 37.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG