Shugaban masu alhakin dauka da nada sabon sarki, Barista Ibrahim Birma, ya ce lallai ne za a dauki wanda zai gaji marigayin, amma a yanzu basu kamala zub da hawaye na rashin wannan sarkii dake matsayin uba a gare su ba. Dan haka ba zasu yi gaggawa a kan wanene zai ko wanene ba zai hau sarautar ba.
Barista Birma, ya yabawa kyawawan halayen marigayin inda yake masu nasiha a kan da’a, nasihar da ya ce ta amfani rayuwar su. Ya kuma kara da cewa ya zuwa yanzu bai wata tattaunawa da kowa da kowa ba a kan batun sarauta.
Marigayi sarkin Biu, Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu, ya rasu ne a daren ranar Litinin a babban asibitin koyarwa na tarayya a Gombe bayan gajeruwar rashin lafiya a cewar gwamnatin. Ya cika yana da shekaru 80 a duniya.
Mai martaba sarkin Biu wanda tuni aka yi jana’izar sa, ya bar mata hudu da ‘ya’ya sittin da shida da kuma jikoki saba’in da uku,
Sarkin Biu Aliyu wanda ya hau kan karagar mulkin Biu a shekarar 1989, ya sha yabo daga al’ummar yankin da suka bayyana rasuwar shi da babban rashi. Haka suma matasa suke yabawa aikin sa na ganin ya kyautata rayuwar su, inda wasu matasa ke fadin cewa Sarki Aliyu na daukar matsalar matasa tamkar matsalar kansa ne.
Ga rahoton Harun Dauda Biu
Facebook Forum