Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masar zata binciki kashe mutane ashirin da hudu da aka yi

Wata Musulma ta taga Alkura'ani mai girma a lokacin da ita shiga zanga zangar goyon bayan yan uwantaka ga zanga zangar da Kiristoci yan darikar Coptic suka yi.
Wata Musulma ta taga Alkura'ani mai girma a lokacin da ita shiga zanga zangar goyon bayan yan uwantaka ga zanga zangar da Kiristoci yan darikar Coptic suka yi.

Majalisar mulkin soja ta kasar Masar ta baiwa gwamnati umarnin ta binciki kashe akalla mutane ashirin da hudu da aka yi a mumunar fafatwar da aka yi ranar lahadi tsakanin Kirista yan darikar Coptic da jami’an tsaro a birnin Alkahira.

Yau litinin Majalisar mulkin soja ta bada wannan umarni bayan ta tattauna akan wannan rikici, wadda itace tarzoma mafi muni da kasar ta gani, tun rikicin watan Fabrairu data hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Hosni Mubarak. Sojojin da suka karbe ragamar mulki daga hannun Mubarak sun kuma jaddada alkawarin da suka yi na mika mulki hannun farar hula bayan anyi zabe a kasar.

An fara arangamomin ne, bayan da fiye da Kirista dubu daya da magoya bayansu suka yi jerin gwano zuwa gidan talibijin na kasar a birnin Alkahira domin nuna rashin amincewarsu ga harin da wasu Musulmi masu tsatsauran ra’ayi suka kai kan wani coci a kudancin kasar.

Zanga zangar sai ta buge da zama tarzoma, a lokacinda masu zanga zangar suka fara fafatwa da sojoji wadanda suke gadin gidan talibijin din. Shedun ganin da ido sunce sojojin sun kutsa ta kan masu zanga zangar da motocin yaki, suka kashe da dama daga cikinsu. Wasu mutane kuma sun jejefi jami’an tsaro da duwatsu da kuma bama baman da aka yi da kanazir.

Yawancin wadanda aka kashe yan darikar Coptic ne. Akalla sojoji uku suna daga cikin wadanda aka kashe.

Fadar shugaban Amirka tace, shugaba Barack Obama ya damu ainun dangane da rasa rayukan da aka yi, kuma yayi kira ga bangarorin da su kai zuciya nesa. Shi ma baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya gabatar da sanarwar yana nuna damuwa akan barkewar tarzomar.

Su dai iristocin kasar Masar suke zaman kashi goma daga cikin dari na al’ummar kasar miliyan tamanin.

XS
SM
MD
LG