A yau Alhamis wata kotun kasar Uganda ta tuhumi wasu jami’an gwamnati ukku da suka yi murabus jiya-jiyan nan, da laifin rashawa da cin hanci.
Lauyoyin gwamnati masu shigar da kara sun tuhumi tsohon ministan harakokin waje Sam Kutesa, da tsohon karamin ministan kwadago Mwesigwa Rukutana da kuma John Nasasira wanda ya taba yin kakakin majalisar dokoki sau daya, an tuhume su ne da laifin yin amfani da mukaman su fiye da kima, da kuma janyowa gwamnati asarar kudi.
An tuhume su ne dangane da wasu kudade kusan dola miliyan biyar da suka yi layar zana daga asusun gwamnati a shekarar dubu biyu da bakwai, lokacin da kasar Uganda ta shirya taron shugabannin kasahen Kungiyar Kwamanwels.
Jami’an gwamnatin sun yi murabus ne a jiya Laraba a gabannin zuwan su kotun hukunta laifuffukan rashawa da cin hanci, amma su na kan bakan su cewa ba su aikata laifin ba.
Su ka ce sun yi murabus ne domin su baiwa kotu damar kammala aikin ta, kuma sun yi ne saboda ci gaban gwamnati da jam’iyyar da ke mulki.
Jami’an gwamnatin su na fuskantar daurin shekaru har goma sha ukku-ukku a kurkuku idan aka same su da laifi.