Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masar Ta Ce Ta Kashe 'Yan Ta'adda 16


Sojojin Masar yayin kaddamar da hare-hare kan 'yan ta'adda
Sojojin Masar yayin kaddamar da hare-hare kan 'yan ta'adda

A wani gagarumin mataki na fatattakar 'yan ta'adda, sojoji da 'yan sandan kasar Masar sun ce sun yi rugu-rugu da makaman 'yan ta'adda da sauran kayan aika-aikarsu baya ga kashe wasu 16 daga cikinsu da kuma damke 30 da su ka yi.

Yau dinnan Lahadi, Rundunar Sojin Masar ta ce ta hallaka wasu ‘yan bindiga 16 sannan ta kama wasu da ake zargi su wajen sama 30 a wani aikin kakkabe ta’addanci wanda ta kaddamar a makon jiya, inda ta auna ‘yan ta’adda da sauran miyagu da kungiyoyinsu a fadin kas

Kafar labarai ta Reuters ta ce mai magana da yawun Rundunar Sojin, Kanar Tamer el-Rufai, ya fadi yau Lahadi cewa an auna motoci da makamai da na’urorin sadarwa da ma gonakin tabar sa maye ta opium a wannan aikin.

A wani jawabinta da aka yada ranar Jumma’a ta gidan talabijin, Rundunar sojin ta ce da sojoji da ‘yan sanda duk sun taka rawa a abin da ta kira “tsararren samame.”

Wannan aikin tsaron ya mai da hankali ne kan yankin Sinai mai fama da tashin hankali, inda a bara ‘yan bindiga su ka kai hari kan wani masallacin Sufaye, su ka kashe masu ibada wajen 311.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG