Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

In Anyi Kokari, Hukumar NEDC Zata Kawo Sauyi A Rayuwar Mutanen Arewa Maso Gabas


A cikin watan Oktoba na shekarar da ta shige, 2017, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya rattaba hannu a kan dokar da ta kafa Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas, NEDC a takaice. Aikin hukumar shine ta jagoranci sake ginawa da kuma raya yankin wanda ya lalace kusan baki dayansa a sanadin rikicin Boko Haram.

Masana irinsu David Kieghe, wanda kwararre ne a kan harkokin raya kasa, kuma ya taba rubuta wani littafi mai suna “National Ambition: Reconstructing Nigeria" su na da ra'ayin cewa wannan hukuma zata iya yin tasiri mai kyau idan har ba za a bari ta kauce daga kan hanya ba.

A cikin wata makalar da ya rubuta a shafin yanar gizo na Majalisar Hulda da Kasashen Waje ta Amurka, Mr. Kieghe yayi bayanin cewa ita wannan hukuma ta NEDC zata samu kudaden gudanar da ayyukanta ne ba wai kawai daga gwamnatin tarayyar Najeriya ma, har ma da cibiyoyin kasashen waje kamar Hukumar Tallafawa kasashe Masu tasowa ta Amurka, USAID, Bankin Raya Kasashen Afirka, Bankin Duniya, Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe masu ba Najeriya tallafi.

Sai dai masanin yace a yanzu haka akwai daruruwan kungiyoyin agajin dake aiki a arewa maso gabashin Najeriya. Babban kalubalen da hukumar zata fuskanta shine yadda zata hado hancinsu wuri guda, ganin cewa kowace kungiya alkiblarta dabam. Wani kalubalen kuma shine tabbatar da cewa irin ayyukan da wadannan kungiyoyin suke yi ba su saba da al'adun mutanen yankin ba.

A saboda haka ya bayar da shawarar cewa hukumar NEDC ta yi kokarin hada hannu da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomin yankin wajen tsarawa da zayyana ayyukan kungiyoyin agajin. Ta kuma hada kai da ofishin ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya wanda shi ma yana gudanar da ayyuka a wannan yankin.

Tuntubar mutanen yankin wajen tsara ayyukan wannan hukuma yana da matukar muhimmanci domin a tabbatar da cewa ana takalar bukatunsu.

David Kieghe yayi hasashen cewa idan aka aiwatar da tsarin wannan hukuma ta NEDC cikin nasara kuma kamar yadda ya kamata, to la shakka, zata kawo sauyi a rayuwar al'ummar dake zaune a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG