Bankin Duniya ya ce lallai bullar annobar COVID-19 da kuma mummunan faduwar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya zai jefa Najeriya a cikin mawuyacin hali, sai dai idan akwai matakin da za a dauka nan da watan tara na shekarar nan ta 2020.
Wannan bayani ya sa mahukuntan kasar daukar matakin bada tallafi a yayin da Majalisar Zartarwa ta kasar ta bada umurnin fitar da kudi har Naira tiriliyan 2.3 domin yin wannan aiki.
Sai dai kwararre a fanin tattalin arziki na kasa da kasa, Shu'aibu Idris Mikati, ya ce da sauran rina a kaba domin ba a fayyace bangarorin da za a taba da kudaden ba, saboda haka ya na ganin ba zunzurutun kudin za a fitar ba tunda ba a aika da kasidar kashe kudin zuwa majalisar dokokin kasa ba.
Shi ma Shugaban Hukumar Kula da Kananan Masana'antu da Matsakaita, Dikko Umar Radda, ya ce hanya daya ce ya kamata a bi wajan tallafa wa masu kananan masana'antu idan ana son tattalin arzikin kasar ya bunkasa.
Ya kuma kara da cewa wannan hanya ita ce a ba su tallafi na gudanar da kasuwancinsu ba tare da neman sai sun biya kudin tallafin ba, saboda an kwashi lokaci mai tsawo ba a mu'amala da kudi sakamakon haka kasuwancin kananan masana'antu ya durkushe, sai an tada su.
Kafin bayyanar annobar COVID-19 an yi hasashen tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa da kashi 2.1 cikin 100 a wannan shekara ta 2020 a cewar wani rahoto na Bankin Duniya.
Yanzu dai ana zuba ido a gani ko wannan tallafin zai yi tasiri cikin dan kankanin lokaci wajan farfado da tattalin arzikin Najeriya da ya ta'allaka kan danyen man fetur.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Facebook Forum