Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana ilimin hasashen yanayi sun hango karin ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar Pakistan


Masanan kasar Pakistan masu ilimin hasashen yanayi sun hano karin ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar wadda ambaliyar ruwa ta riga ta daidaita.

Jami’an gwamnatin kasar Pakistan sun ce ambaliyar ruwan da ta yi kaca-kaca da yankin arewa maso yammacin kasar ta rutsa da mutane miliyan 13 a kalla, kuma yanzu haka ambaliyar ruwan ta nufi kudancin kasar, al’amarin da ya tilastawa karin wasu dubban mutane tserewa daga gidajen su.

Shugaban hukumar ceton gaggawa ta kasar, Nadim Ahmed ya fada a jiya Jumma’a cewa a lardunan arewa maso yamma na Khyber Pakhtunkhwa da kuma Punjab ta tsakiya gidaje dubu 650 ne su ka lalace su ka bi ruwa.

A lardin Sindh na kudancin kasar, tuni dai har hukumomin kasar sun kwashe mutane fiye da rabin miliyan daya.
Bala’in da kusan makonni biyu kenan da ya afkawa yankin, ya halaka mutane fiye da dubu daya da dari shidda. Ambaliyar ruwan ta tafi da gidaje da hanyoyi da gadoji, ta katse zuwa da komowa tsakanin garuruwa.

‘Yan kasar Pakistan masu dimbin yawa na ci gaba da sukan nuna rashin yabawa da sanyin jikin da gwamnatin kasar ta yi wajen daukan matakan kai dauki, haka kuma shugaban kasar Asif Ali Zardari ya na shan bambami saboda ci gaban da ya yi da rangadi a Turai a lokacin da ‘yan kasar ke fama da bala’in ambaliyar ruwa.

XS
SM
MD
LG