Babbar jam’iyyar siyasa a Kudancin Sudan ta ce ya kamata a gudanar da kuri’ar raba-gardama kan ko yankin zai zamo kasa mai ‘yancin kai a cikin watan Janairu kamar yadda aka tsara, koda kuwa ba a kammala shata bakin iyakar yankin da kuma Arewacin Sudan ba.
Amma jami’ai da shugabanni na Arewaci sun ce bai kamata a gudanar da kuri’ar ba har sai an kammala shata bakin iyakar yankunan biyu.
A wannan makon, rikici ya sake kunno kai game da yankin Abyei mai arzikin albarkatun kasa, duk da hukumcin da wata kotun duniya ta yanke kan yankin a shekarar da ta shige. A watan Yulin 2009, Kotun Dindindin ta Sasantawa ta Duniya ta yanke hukumci kan bakin iyakokin Abyei a bisa rokon jam’iyyar SPLM ta Kudancin Sudan da kuma jam’iyyar NCP mai mulkin kasar a yanzu.
Hukumcin ya bayar da akasarin albarkatun man fetur na Abyei ga Arewa, amma ya ba yankin kudu damar mallakar yankuna masu yawa dake da mai da kuma na noma idan har masu jefa kuri’a na Abyei suka zabi ballewa su bi Kudu a wata kuri’ar dabam da za a yi a wannan yanki.
Jami’an kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci sassan da su warware duk sabanin dake tsakaninsu kafin wannan zaben raba gardama da aka shirya gudanarwa a ranar 9 ga watan Janairun 2011.