Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da wata tawaga don yin ta’aziyya ga iyalai da abokan fitaccen mawakin Hausa Isyaku Mohammed wanda aka fi sani da Forest.
Wata sanarwa wacce kakakin shugaba Buhari Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi ta ce shugaba Buhari ya kwatanta rasuwar Forest a matsayin “babban rashi” ga fannin siyasa da kuma raya al’adu.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa Forest ya taka muhimmiyar rawa wajen yi masa kamfen da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A ranar 4 ga watan Satumbar 2021 Forest ya rasu.
A 2020, an taba yanke masa kafa bayan tsawon lokaci da ya kwashe yana fama da jinyar kafar.
“Wakokinsa da na sauran abokanan sana’arsa sun jawo hankulan mabiya wadanda suka ci gaba da yin amanna da jam’iyya.
“Zai ci gaba da kasancew a zukatanmu har abada. Ina mai mika sakon ta’aziyya ga iyalansa, abokanai da masu sha’awar wakokinsa.” Sanarwar ta ce.
Forest ya taka rawa wajen wakokin da mawakan Kannywood suka yi wa shugaba Buhari a lokutan zabe daban-daban da kuma sauran ‘yan takarar jam’iyyar.
Fitacciyar wakar da Forest da ya fito a ciki wacce aka yi wa Buhari da jam’iyyar APC ita ce “Gaskiya Dokin Karfe.” wacce ta samu karbuwa a wajen masoyan jam’iyyar gabanin zaben 2019.
Sun kuma sha yin wakokin siyasa da fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara.