A Jamhuriyar Nijar, kungiyar ADPD mai zaman kanta ta rarrabawa mata da marayu da gajiyayyu kayayyakin abinci a Yamai, da nufin sassauta wahalhalun da jama’a ke fuskanta a wannan lokaci da cimaka (abinci) ke kara tsada a kasuwanni.
Kungiyar ta ADPD, ta yi amfani da wannan dama don attajiran kasar su yi koyi da irin wadanan ayyukan ceto, kwatankwacin yadda takwarorinsu na kasashen waje ke yi akai-akai.
Daruruwan magidanta galibi mata masu rikon marayu, da wadanda karfinsu ya kare ne, suka amfana da taimakon cimakar da kungiyar ta fara rarrabawa masu karamin karfi.
A unnguwar Tallague inda aka kaddamar da wannan taron, tan 40 na shinkafa ne aka zo da su domin shafe hawayen talakawa.
A Farkon saukar damina lokacin ne da farashin abinci ke matukar hauhawa a Jamhuriyar Nijar, saboda haka kungiyar ta yanke shawarar fadada ayyukan bayard a taimako zuwa wasu sassan kasar, don ganin sauran jama’a ta mori wannan shiri.
Ga cikakken rahoton Wakilin Muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma
Facebook Forum