Asabar idan Allah ya yarda ake sa ran manyan kasashen duniya zasu yi kokarin rage sabanin ra'ayinsu akan batun Syria, a lokacinda zasu fara zagaye na biyu na shawarwari akan kafa jadawalin zartar da wani kuduri a siyasance domin kawo karshen yakin basasar kasar ta Syria.
Ana sa ran cewa shawarwarin da ake yi a birnin Vienna zasu maida hankali wajen gano kungiyoyin kasar masu sassauci ra'ayin da kuma wadanda ake zato ko kuma aka dauka na 'yan ta'ada ne.
Kila Amirka da kawayen ta su yi kokarin magance sabanin ra'ayin dake tsakaninsu da Rasha da kuma Iran akan makomar siyasar shugaba Bashar Al Assad. Nasara kalilan suka samu a zagaye na farko na shawarwarin da suka yi a watan jiya.
A lokacinda aka kamalla zagayen farko na shawarwari, ranar talati ga watan Oktoba, sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, yace dashi da takwarorin aikinsa na Rasha da Iran Sergei Lavrov da Zarif da kuma sauran jami'ai sun cimma daidaituwa sa'anan kuma suka samu saba'in ra'ayi.
Rasha da Iran suna goyon bayan gwamnatin Bashar Al Assad. ita kuma Amirka ta tsaya kai da fata cewa tilas shugaba Assad ya sauka dagan kan ragamar mulki kafin a samu wani kudurin kawo karshen yakin basasa a kasar.
Asabar idan Allah ya yarda ake sa ran manyan kasashen duniya zasu yi kokarin rage sabanin ra'ayinsu akan batun Syria.