Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce bangaren shugaban kasar Libiya Moammar Ghadafi ma ya san cewa zamanin shugaban ya kawo karshe, a daidai lokacin da kasa da kasa ke dada zafafa matsin lamba a kan gwamnatin shi.
A cikin wata hirar da aka yi da shi a talbijin jiya talata, shugaba Obama ya ce azargagi na kara zarge Mr. Ghadafi, kuma wadanda ke tare da shi sun san fara yarda da cewa tura ta kusa kaiwa bango. Mr. Obama ya ce yanzu kasa da kasa na bukatar zafafa matsin lambar diflomasiyya ta yadda shugaban kasar Libiya zai yanke shawarar tattara na shi ya na shi ya bada wuri.
Sama da mako daya kenan da sojojin kasa da kasa ke ta ruwan wuta akan sojojin Ghadafi da nufin karfafa shamakin tsaron da MDD ta bada izinin shatawa a sararin samaniyar kasar Libiya. Haka kuma manyan kasashen duniya sun aiwatar da matakan tsuke bakin lalitar gwamnatin kasar Libiya.
A wajen wani babban taron da aka yi jiya talata a London babban birnin kasar Birtaniya, ministocin harakokin wajen kasashe fiye da arba’in da kungiyoyin kasa da kasa sun cimma jituwar cewa dole ne Mr.Ghadafi ya yi murabus a daidai lokacin da su ke zafafa tattaunawa da ‘yan adawar kasar Libiya domin a yi canjin gwamnati a kasar ta yankin arewacin Afirka.
Sakatariyar harakokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta fada cewa kudirin MDDr da ya bada izinin karfafa tsaron sararin samaniyar kasar Libiya, zai bada dama kasashe su baiwa ‘yan tawayen Libiya makamai akan ka’ida, duk da cewa ba a yanke shawarar yin hakan ba. Ministan harakokin wajen kasar Faransa, Alain Juppe, ya ce gwamnatin kasar shi a shirye ta ke ta tattauna akan yadda za a isar da taimakon makamai ga masu adawa da Ghadafi.
Amma a yau laraba ministan harakokin wajen kasar Rasha, Sergei Lavrov, ya yi kashedi game da bada makamai ga masu adawar. Ya ce gwamnatin kasdar Rasha ta yarda da furucin da babban magatakardan kawancen tsaron NATO, Anders Fogh Rasmussen ya yi cewa, aikin da ake yi a kasar Libiya, ana yi ne domin a kare lafiyar al’umma, ba don a yi mu su damarar yaki ba.