Ana kyautata cewar shugaba Robert Mugabe Zimbabwe da Friminista Morgan Tsvangirai zasu gana da shugabannin kasashen Afirka a taron kolin da ake yi a Livingstone na kasar Zambia.
Shugaba Mugabe yhayi kiran da a gudanar dazabe a karshen wnanan shekarar, duk da rashin nuna amincewar da Mr. Tsvangirai ke nunawa wajen kin goyon bayan ayi zaben bisa hujjar cewa kafin ayi sabon zabe, ya akamata a Zimbabwe ta tabbatar da samun yanayin zabe na gaskiya cikin adalchi da lumana tukuna.
Kasashen Afirka goma sha biyar ne na kungiyar SADC ke karfafa aiki da yarjejeniyar zaman lafiya ta daunin iko a kasar Zimbabwe domin a kawo karshen rikicin day a biyo bayan zaben shugaban kasar daaka gudanar a shekarar 2008. Sauran kasashen dake halaartar taron kolinsun hada da shugaba Zambia, da na Afirka ta kudu, da na Mozambique, da kuma Namibia.