Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manufofin ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Na Ghana Ta Fannin Tattalin Arziki


Zaben Ghana
Zaben Ghana

‘Yan takarar shugaban kasa na manyan jam’iyyun kasar Ghana, Dr. Mahamudu Bawumia na jam’iyar NPP da kuma Dr. John Dramani Mahama na jam’iyar NDC, na ci gaba da yayata manufofinsu da ayyukan da za su yi wa kasa idan ‘yan Ghana suka zabe su.

A bangaren tattalin arziki, Dokta Bawumia ya ce Ghana na bukatar a ginata ta hanyar ‘tattalin arzikin Dijital’, shi kuma Dokta Mahama ya ce Ghana na bukatar a kara saita ta, ta hanyar, ‘tattalin arziki na awa 24’.

Shin ko me suke nufi? Kuma ya al’ummar Ghana suka amshi wadannan manufofi nasu? Idris

Dokta Mahamudu Bawumia ya ce Ghana na bukatar a ci gaba da gina ayyukan da suka fara yi da shugaba Akufo-Addo, ta hanyar tsarin ‘tattalin arziki na fasahar digital’, wanda ke da alaka da kowane gida, kowane ofishin gwamnati, kowace makaranta da kowane kasuwanci.

Mahamadu Bawumia
Mahamadu Bawumia

Sadat Yahaya Baako, jam’in sadarwa ne na jam’iyar NPP, ya yi wa Muryar Amurka karin bayani kan tsarin tattalin arziki na digital.

“Dokta Bawumia ya mayar da hankali kan gudanar da aiki cikin sauki, ta amfani da fasahar zamani.” Ya kara da cewa, tsarin digital zai magance cin hanci da rashawa domin kudade ba su bin hannun mutane."

"Yau idan aka kawo digital aka yi amfani da shi, wa za ka gani balle ka ba kudi. Ka ga an magance ‘cin hanci da rashawa’ a nan, kuma za a sami saukin rayuwa a cikin lamarin mutane," a cewar Sadat.

Yakin neman zaben Bawumia
Yakin neman zaben Bawumia

Shi kuma Dokta John Mahama yace, Ghana na bukatar tsarin ‘tattalin arziƙin sa'oi 24’, wanda ke da aniyar habbaka yawan aikin yi ta hanyar fadada harkokin kasuwanci, ayyukan jama'a, da duk harkokin samun kudi, babu kakkautawa, tsawon awa 24 a rana.

Alhaji Mohammed Nazir Saeed, shi ne daraktan sadarwa na jam’iyar NDC da ke kula da yankin Zango, a karin bayaninsa kan manufar ‘tattalin arziki na sa'oi 24’, ya ce tsarin zai samar da aikin yi ga matasa, sannan kuma ya bude hanyar kara darajar kudin Ghana, domin za a samu habbakar kirkirar kayayyakin da za a fitar da su kasashen waje, hakan kuma zai kara darajar kudin Ghana.

John Dramani Mahama
John Dramani Mahama

Kamar yadda masani kan harkokin zabe, kuma shugaban kamfanin bincike mai zaman kansa, na InfoAnalitics, Mussa Dankwa ya bayyana, bayan binciken ra’ayin jama’a da suka yi kan wadannan manufofin na tattalin arzikin awa 24 da na digital, sun gano cewa duk matasa da dattijai, wadanda ba su bayyana jam’iyar da suke bi ba, da kuma wadanda ba su da jam’iyyar, sun nuna cewa sun fi amincewa da tattalin arziki na awa 24. Mabiya jam’iyar NPP ne kawai suka fi amincewa da tattalin arziki na digital.

Yakin neman zaben Mahama
Yakin neman zaben Mahama

Kamar yadda wasu masana suka ce, duk wanda ya yi nasara a zaben nan, to ya hada tsarin tattalin arzikin digital da na sa'o'i 24 ya aiwatar, domin dukkansu suna da muhimmanci ga ci gaban kasa; suna da fa'ida da za su iya tsara makomar Ghana ta hanyoyi dabam-dabam.

Saurari rahoton Idris Abdullah Bako:

Manufofin ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Na Ghana Ta Fannin Tattalin Arziki
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG