Kungiyar makiyaya da ake kira AMPEN a takaice, a Janhuriyar Nijar, da hukumomin Jihar Tahoua sun shirya wannan taron ne don tattauna matsalolin da ake samu tsakanin makiyaya da manoma.
Dakta Usman Sumaila, Magajin garin birnin Konni yace wannan taron da aka shirya faduwa ce ta zo daidai da zama. Saboda yankin na fuskantar rikici tsakanin makiyaya da manoma duk lokacin da damina ta zo karshe. Ya kuma ce a kullum suna cikin fargaba, har sai lokacin da manoma suka kwashe amfanin gonarsu.
An dai shirya wannan taron ne don neman hanyar samun zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya, da kuma ilimintar da al’ummomin biyu akan dokar kasa, a cewar malam Abdalla, shugaban kungiyar makiyayan da ta shirya wannan taron.
Mataimakin gwamnan jihar Tahoua, da shugabannin gargajiya da kungiyoyi dabam dabam ne suka halarci taron mahawarar.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum