A karshen wani binciken da jami’an asusun bada lamuni na IMF suka gudanar asusun ya bayyana gamsuwa da yadda hukumomin jamhuriyar Nijar, suka tafiyarda kudaden tallafi a shekarar 2017, abinda ya sa ake hasashen tattalin arzikin kasar zai bunkasa a shekarar 2018 sai dai masana na cewa yanayin rayuwar da talakkawa ke ciki a yau shine ma’uni mafi inganci wajen tantance halin fatarar da kasar ke fama da ita.
Makoni akalla biyu tawagar jami’an asusun na IMF, ta shafe dana gudanar da bincike akan yadda hukumomin Nijar, suka tafiyarda kasafin kudaden shekarar dake shirin karewa daga tallafin kasashen waje da wadanda kasar ta samu daga cikin gida.
Ministan kudin jamhuriyar Nijar, Hassoumi Massaoudou, yace Nijar, ta bi duk ka’idojin da suka kamata shi yasa sanarwar da tawagar ta bayar ke cewa asusun lamuni ya gamsu da yadda Gwamnatin Nijar, ta tafiyarda harkokin kudi a shekarar 2017.
Masana a fannin tattalin arziki irin su Dr. Ibrahim Soli, na ganin aiwatar da bincike da bayanai na hakika daga mazauna karkara ita kadai ce hanyar da zata bayar da damar tantance zahirin halin da sha’anin tattalin arzikin kasa ke ciki.
Ya kara da cewa kamata yayi idan aka samu bayani daga bangaren gwamnati sai kuma a samu daga bagaren al’umar kasa domin amfani dashi a matsayin mizani da abinda ita kanta ta gaini shi sun sabawa juna ko kuwa a’a.
Facebook Forum