Jebun takin zamani na ci gaba da zama babbar barazana a bangarori dabam-dabam a Najeriya lamarin da ke kawo cikas wajen samar da amfanin gona kamar yadda ya kamata.
Kungiyar manoma a Neja sun koka game da rashin hukunta duk wanda aka samu yana sayar da jebun taki.
"Gaskiya idan ba a dauki mataki ba to akwai matsala," inji shugaban kungiyar manoman, Alhaji Shehu Galadima.
To sai dai Gwamnatin jihar Neja ta ce tana daukar matakin dakile duk wata cuwa-cuwar takin da kawar da masu sayar da jebun taki.
Kwamishinan gona na jihar, Alhaji Haruna Nuhu Dukku, ya musanta cewa ana samun taki na jabu don a cewarsa, gwamnatin jihar ta samar da tsari mai kyau da kamfanin taki ta yadda ba takin da ke barin kamfani zuwa kanana hukumomi sai an raka da jami'an tsaro har sai an kai an sauke.
A karshen makon da ya gabata, an yi ta yayata labarin samun katafaren masana'antar da ke hada taki na jabu a cikin garin Minna, amma kwamishinan ya ce labarin kanzon kurege ne.
Facebook Forum