WASHINGTON, DC —
Tun da ya fito daga gidan kaso Manjo Al-Mustapha ya cigaba da zagayawa kasar Najeriya yana haduwa da al'umma daban daban da shugabannin addinai daban daban.
Tsohon dogarin tsohon shugaban kasa marigayi Sani Abacha, Manjo Al-Mustapha ya ce ya zama wajibi addinai daban daban su hada kai a kasar Najeriya domin tabbatar da cigaban kasar. Manjo Al-Mustapha wanda ya kai ziyara a kudancin Kaduna dake fama da tashe tashen hankali cikin 'yan kwana kwanan nan ya ce ya kamata addinai daban daban su hada kai domin haka Allah ya yi kasar. Allah ya yi kabilai daban daban da yare daban da daban da addinai daban daban. Don haka ya kamata mutane su fahimci cewa suna da bukatar su zauna lafiya domin kawo cigaba.
A jawabinsa Manjo Al-Mustapha ya ce idan suka rabu haka shaidan yake so haka ma mukarraban shaidan suke so. Ya ce ko Musulmi ne kai ko Krista ne kai ka san mene zaman lafiya. Zaman lafiya yana cikin abun da Najeriya ta dogara akai da sunan abun da ta rike. Ya ce ko a Littafi Mai Tsarki Krista ya san ma'anar zaman lafiya. A Kur'ani ko Hadishi Musulmi ya san ma'anar zaman lafiya. Ya ce ma'anar Islam ma wannan ya isa. Ya ce kowane irin mutum, Musulmi da Krista Allah ba ya barin kowa. Ya kira mutane su yi hakuri da juna su zauna lafiya. Ya ce Allah ya haliccemu tare ya samu a wuraren da ya so don haka a yi hakuri da juna.
Shi kuma shugaban 'yan kasar kudancin Kaduna Mr. Ephraim Goje ya kira wadanda suke kaunar Najeriya, Krista da Musulmai da kowane yare su gyara kasar Najeriya. Ya juya kan matasa ya ce idan muka bari aka bata mana kasarmu, ku sani baku da wata kasa idan ba Najeriya ba. Ya ce su tona asirin masu yin siyasar yaudara wadanda suke labewa da kabilanci ko addini su rura wuta su yi anfani da matasa.
Ga rahoto.