WASHINGTON, DC —
Tsohon babban jami'in tsaron lafiyar tsohon shugaban kasar Najeriya marigayi janar Sani Abacha, wato Manjo Hamza Almustapha ya fito fili balo-balo, yayi bayani karara, ya musanta zargin da ake yi mi shi cewa ya na share fagen siyasa ta hanyar tattara matasa a karkashin sabuwar kungiyar hada kan 'yan kasar Najeriya, kamar dai yadda za ku ji a cikin wannan rahoto da wakilin Sashen Hausa Isah Lawal Ikara ya aikodaga Kaduna.
Hamza al-Mustapha Ya Ce Ba Ruwan Shi Da Siyasa

Manjo Hamza al-Mustapha ya ce shi fa ba yau ya fara taimakawa matasa ba