A ranar 29 ga watan nan na Yuli, ‘yan kasar Mali za su garzaya zuwa rumfunan zabe, domin yin zabi tsakanin ‘yan takara 24, wadanda suke neman mukamin shugaba kasa.
Babu ko da ya daga cikin ‘yan takarar, ciki har da shugaba Ibrahim Boubacar Keita da shugaban ‘yan adawa Soumaila Cisse, da ake sa ran zai yi nasara ta hanyar samun kuri’u masu rinjaye kai-tsaye.
Hakan ya sa ake ganin akwai yiwuwar sai zaben ya kai ga zagaye na biyu.
Sara Coulibaly, Malama a wata unguwar marasa galihu a Bamako, ta ce, ita damuwar ita ce, duk wanda ya ci, ya taimaka ya sauke farashin kayan abinci.
Facebook Forum