“Ni ne Olivier Dubois. Ni Bafaranshe ne kuma dan jarida ne. JNIM (ƙungiyar da ke da alaƙa da al-Qaeda) ne suka sace ni a Gao ranar 8 ga Afrilu. Ina kira ga iyalai na, abokaina da hukumomin Faransa don su yi duk abin da za su iya su ‘yantar da ni,” in ji Dubois a cikin bidiyo na sacan 21 da aka yada a shafukan sada zumunta.
Ba a dai tabbatar da sahihancin bidiyo ba nan take.
Wata majiyar ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da bacewar dan jaridar kuma ta ce ma’aikatar tana kan magana da danginsa tare da gudanar da bincike na fasaha kan sahihancin bidiyon.
Kawo yanzu, ba a samu bayanai daga hannun hukumomin Mali ba.
Dubois shi ne Bafaranshe na farko da ‘yan tawaye suka yi garkuwa da shi a Mali tun bayan da aka sako‘ yar aikin sakai ta Faransa, Sophie Petronin a watan Oktoban bara. An sace ta ne a kusa da Gao a ƙarshen 2016.