Kamar yadda mataimakin limamin babban masallacin garin Jos Malam Muhammad Gazali Ismail Adam yace lokacin azumi lokaci ne da al'ummar musulmi ya kamata su bi duk abubuwan da Allah ya halatta da kuma kaucewa wadanda ya haramta.
Yace watan Ramadan ya kunshi tarbiya ne ga rayuwar musulmi. Idan mutum ya shiga watan yana komawa ga Madaukakin Sarki ya duba dukan abun da ya halarta da kuma ya haramta ya kauce masu. Daya daga cikin abubuwan da Allah ya haramta shi ne ci da sha a wasu lokutan rana lokacin azumin.
Liman Adam ya ce fa'idodin watan suna da dama. Na farko zai sa mutum ya zama mutumin kirki. Zai karawa mutum hakuri. Mutum zai san na gaba da dashi da abun da ya dace yayi.Lokaci ne kuma na kusantan Allah. A jiki ma mutum na zama lafiyayye. Yunwar azumi na sa mai hannu da shuni ya dandana irin abun da talaka ke fama dashi ya kuma zama mai tausayi.
Duk wanda ya ki ya yi azumi da gangan a watan Ramadan to ko ya fita daga addinin musulunci.
Liman Adam ya kira masu yin tafsiri su kula da irin lafuza da ake anfani dasu.Yace su yi kira ga zaman lafiya da hadin kai, a zama tsintsiya madaurinki daya ba tare da tsangwama ba.
Sani Suleiman Maigoro shugaban matasan musulmai yace kamata yayi matasa su yi anfani da darusan watan Ramadan wajen gina zamantakewa da gyara kurakuran da suka yi saboda gina Najeriya. Misali wasu abubuwa da suke sha idan sun bari a watan Ramadan me zai hanasu cigaba da gujewa wadannan abubuwan da Allah Ya haramtasu.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.