A shirin mu na mata wakiliyar DandalinVOA tayi hira da Malama Uwani Muhammad Kabuga mai sana’ar abinci, in da tace ta zama mai dogaro da kai.
Bayan rasuwar mai gidan ta, ta fara sana’ar abinci duk da cewar ‘ya'yan da ya bar mata basu rasa ci da sha ba.
Ta ce ta fara sana’ar ne shekaru goma da suka wuce, ta fara da dafa shinkafa rabin kwano, har ta kai a yanzu a sana’ar, ana dafa abinci daban daban har na kusan dubu hamsi zuwa dubu sittin a kowacce rana.
Ta sana’ar hannu sana’a ce da ke bukatar hakuri da juriya, kuma da kadan ake fara wa har ta kai ga zama babba. Hajiya Uwani ta ce baya sana’ar abinci tana sana’ar hajja a cikin gida inda take tare da ‘yayanta.
Hajiya Uwani ta kara da cewa yawan roko bashi da amfani kuma ya kan jawo a gaji da mace. Ta sake bayanin cewa tana fara abincin ne daga karfe takwas na safiya zuwa karfe takwas na yamma a kullun.
Hajiya Uwani dai tana da shago har guda biyu na abinci, sannan tana da kimanin ma’aikata guda takwas da suke yi mata aiki, sannan ta ce da sana’ar ne take kula da kanta har ma ta kula da wasu.
Daga cikin kalubalen da take fuskanta sun hada da rashin jituwa daga wajen abokan sana’a da suke kusa da ita, sai kuma matsala ta bashi.
Ga cikakken rahoton wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.
Facebook Forum