Biyo bayan taron makon jiya hukumar tattalin arzikin Najeriya ta kebe ranaku biyu cikin makon gobe, wato Litinin da Talata ta yi nazari akan abun da ta ji kuma ya kamata kasar ta yi da nufin farfado da arzikin kasar.
Wani kwararre kan tattalin arziki ya duba wannan taron nazarin da za'a yi da abubuwan da yakamata ya cimma ko kuma za'a iya cimma. Malam Yushau Aliyu yace taron ka iya fito da manufofin da zasu iya canza rayuwar 'yan Najeriya.
Yace dole ne a yi maganar tsarin kafa asusu daya da gwamnatin tarayya ta fito dashi da gwamnatocin jihohi inda zasu ajiye kudadensu da zummar canza rayuwar talakawa. Dole kuma taron ya taba karkasuwar raba tattalin arziki da abubuwan da suka fi mahimmanci da gwamnati zata fi kashe kudi a kai.
Yakamata a yi magana akan yadda za'a yi anfani da kudaden da ake kwatoowa daga hannun mutanen da suka wawuresu da.
A nashi bangaren wani masanin tattalin arziki Alhaji Abubakar Ali yace idan ana son taron ya yi tasiri dole ne a fadadashi saboda hukumar tattalin arzikin mutanen gwamnati ta kunsa kawai. Kamata ya yi a kawo masana da 'yan kasuwa cikin taron domin ya yi tasiri.
Tun fil azir taron gwamnoni da ma'aikatan gwamnatin tarayya ya kunsa. Babu abun da zai haifar idan ba'a hada da wadanda zasu fada masu gaskiya ba. Yace yakamata a hada da 'yan kasuwa da bankuna har ma da masu canjin kudi. Tunda taron kasa gaba daya ne a bar mutane kowa ya fito da ra'ayinshi.
Ga karin bayani.