A saukar daminar bana kungiyoyinsu a Nijar sun shiga aikin wayar da kan juna don gujewa rikici a daminar bana.
A yayin da aka sami saukar damina a mafi yawancin yankunan jamhuriyar Nijar, Kungiyoyin makiyaya sun karkatar da ayyukansu ga taron wayar da kan manoma da makiyaya.
Dangane da batun kiyaye burtali domin kaucewa rigingimu tsakanin wadanan al’ummomi mazauna karkara. Kasancewa abin da ya dade yana ciwa bangarori tuwo a kwarya.
Malam Manu Bage jami'i a ma'aikatar noma, shine Sakatare a kungiyar jami'an bunkasa ayyaukan gona a Nijar. Inda ya tabbatar da cewa damina kam ta sauka kusan gaba daya a kasar.
Su ma kungiyar bunkasa kiwo suna kan wayar da kan mutanensu game da burtali ko inda ba burtali ba. Malam Amadu Dangi jigo ne a kungiyar makiyayan wanda ya dada karin bayani.
Wakilinmu a Yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana karin bayani a cikin wannan rahoto cikin murya dake kasa.