Taron ya gudana ne a daidai lokacin da mukaddashin shugaban kasa yake cigaba da ziyara a yankin Niger Delta mai albarkatun man fetur domin yin sulhu da kungiyoyin dake tada kayar baya su daina fasa bututan mai.
Malama Garba Shehu kakakin shugaban kasa ya yiwa manema labaru karin haske akan taron na majalisar zartaswa.
A cikin matakan da za'a dauka Mukaddashin shugaban kasa yace dole ne a jawo 'yankasuwa masu zaman kansu domin su gudanar da harkokin tattalin arziki. Ita ma gwamnati zata bada tata gudummawar domin kawo cigaba.
Sun yadda cewa dole a bunkasa samun wutar lantarki a kasa gaba daya. Nan da shekaru hudu ko biyar ana sa ran kirkiro ayyuka wajen miliyan goma sha biyar.
Akan darajar Nera fitinar Niger Delta da faduwar farashin man fetur suka karyata. Yanzu da fitinar ta fara lafawa kuma farashin mai ya soma hawa sama darajar Nera zata dawo, inji Malam Garba Shehu.
Dangane da bunkasa harkokin noma wanda kashi biyu kacal cikin dari na kasafin kudin kasar aka tanada mashi, Malam Garba Shehu yace baicin kasafin akwai wani shiri na musamman da aka yiwa harkokin noma a kasar.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.