Matakin takaita yawan membobin gwamnati wanda shugaban kasar Nijer ya dauka bayan da ya karbi ragamar mulki a ranar 2 ga watan Afrilun da ya gabata da a daya gefe wasu bukatun da gwamnatin tace sun karu akan wadanda ke kunshe a kasafin shekarar nan ta 2021 ne ya sa majalisar soma wannan zaman domin tantauna wannan bukata ta kwaskware kasafin kudin kasa.
Ganin yadda gwamnatin ta bukaci majalisa ta bata izinin kara yawan kudade akan wadanda kasafin ya kunsa a can farko ya sa bangaren adawa jan hankulan ‘yan majalisar su maida hankali don tabbatarwa kansu an yi abin don talakka inji Honorable Ibrahim Yacouba.
To amma a cewar honorable Boukari Sani Zilly na bangaren masu rinjaye bukatun tallaka ne mafarin bullo da wannan gyaran fuskar.
Gwamnatin da ta shude ce ta tsara kasafin kudin shekarar 2021 wanda kuma majalisar dokoki ta wancan lokaci ta yi na’am da shi a wani lokacin da dukkansu ke gab da kammala wa’adinsu.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: