Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Nijer Ta Amince a Yi Wa Kasafin Kudin 2020 Garambawul


Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijer ta aiwatar da gyaran fuska ga tsarin kasafin kudaden shekarar nan ta 2020, domin bai wa gwamnatin kasar damar tunkarar wasu matsaloli da suka taso.

Bullar annobar cutar coronavirus da ake fama da ita a yanzu haka a daukacin kasashen duniya na daga cikin dalilan da suka sa gwamnatin kasar ta shigar da bukatar kwaskwarimar kasafin kudin a gaban majalisar dokokin kasa.

Sakataren ofishin ministan kudin kasa, Habou Hamidine ya bayyana cewa, bullar annobar COVID-19 ce ta sa gwamnatin kasar ta ke so ta samar da kayayyakin kula da lafiya.

Bayan da bangarorin majalisar suka tafka mahawara akan bukatar gwamnatin kasar, daga bisani sun amince da sauye-sauyen da gwamnatin ta zo da su sakamakon gamsuwa da hujjojinta, a cewar Alio Abdou Saley da ke bangaren masu rinjaye.

‘Yan adawa a majalisar dattawa sun juya wa wannan bukata baya, saboda a cewarsu akwai alamar durba durba a tsarin da gwamnatin ta zo da shi, kamar yadda kakakin ‘yan majalisa na bangaren jam’iyyar hamayya Salifou Hassan ya shaida wa manema labarai. Ya kuma ce ba a yi musu bayanin kason da aka riga aka aiwatar a kasafin kudaden na ainihi ba.

Ya kara da cewa, a ka’ida ya kamata a sanar da ‘yan majalisa adadin kudaden da aka kashe a kasafin kasa, amma ba a yi hakan ba, saboda haka suka juya wa bukatar gwamnatin kasar baya. Ya kuma ce babu hannun su wajen amincewa da sabon kasafin.

Wannan shine karon farko da gwamnatin Nijar ta nuna bukatar aiwatar da sauye-sauyen tsarin kasafin kudaden shekarar 2020.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG