A Jamhuriyar Nijer yau litinin 28 ga watan Satumba ake fara zaman makoki na kwanaki 3 sakamakon rasuwar wasu alhazan kasar a yayin turereniyar da ta hallaka mahajjata sama da 700 ranar Alhamis din da ta gabata a garin Mina akan hanyarsu ta zuwa jifar shaidan.
Kakakin gawamnatin Nijer MARU AMADU ne ya gabatarda sanarwar gwamnatin kasar mai dauke da jerin sunayen alhazan Nijer da turmitsitsin kasar Saudia ya hallaka a safiyar Alhamis din da ta gabata.
A karshen wani taron gaugawa da majalisar ministocin ta gudanar a yammacin Asabar gwamnatin ta Nijer ta bayyana juyayi akan abinda ya faru da alhazan kasar inda sakamakon baya baya yace mutane 22 ne suka rasu daga cikinsu kuma akwai wadanda har yanzu ba a tantance sunayensu ba ballantana yankunan da suka fito.
Haka kuma sanarwar ba ta bayarda adadin wadanda suka ji rauni ba sannan ba a bayyana yawan wadanda suka bace a sakamakon faruwar wannan al’amari ba . To amma domin nuna alhini akan asarar rayukan ‘yan Nijer din da turereniyar ta hallaka gwamnatin kasar ta kebe kwanaki uku na zaman makoki saboda haka za a sasauto da tutoci a fadin kasar a tsawon wannan lokaci domin girmama mamatan.
Ba ‘idin kwamitocin da ta kafa a Niamey da can a Saudia gwamnatin ta Nijer a karshen taron na yammacin Asabar ta aike da ministan cikin gidanta zuwa kasar Saudia domin tattauna shirin dawo da wadanda suka jikkata zuwa gida inji sanarwar.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da wasu alhazan kasar Nijer suka fara dawowa gida a yammacin Lahdi.
Ga Rahoton Souly Mumuni Barma.