A safiyar yau Alhamis ne Majalisar dokokin kasar Isra'ila ta kada kuri’ar akan soke dukan ‘yan majalisar ta, ta kuma yi wani zaben a karo na biyu, wanda ba'a taba yin irin sa ba.
Bayan Firaim minista Benjamin Netanyahu, ya kasa kafa gwamnatin hadin gwiwa.
‘Yan majalisa 74 ne suka goyi baya, wasu kuwa 45 basu amince da kudurin ba, wanda zai soke majalisar, ya kuma bada damar yin zabe a ranar 17 ga watan Satunbar bana.
An ba Netanyahu wa’adin kafa gwamnatin hadin gwiwa, zuwa jiya Laraba bayan da ya lashe zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Afirilun da ta gabata.
Ya sa-ran kafa gwamnatin gamin gambiza tsakanin jam’iyyar sa, da ta masu ra’ayin ‘yan mazan jiya, da ‘yan majalisar kasar masu ra’ayin rikau, sai wata jam’iyyar, masu ra’ayin ‘yan mazan dake karkashin jagorancin tsohon ministan tsaron kasar, Avigdor Lieberman.
Facebook Forum