Wata kungiyar lauyoyi mai lakabi West African Institute for Legal Aid itace ta gabatar da bukatar neman kirkiro da sababbin masarautu a jihar Kano a wata wasikar da kungiyar ta aikewa shugaban majalisar dokokin Kano inda ta fadawa cewa yawan jama’a da fadin kasa suna cikin manyan dalilan samar da karin masarautu a jihar Kano.
Shugaban masu rinjayi a majalisar dokokin jihar Kano, Bappa Babba Danagundi, yace majalisa ta taba kiran wannan doka a baya, ta yi umarni a yiwa dokar gyara ta yanda zata yi daidai da zamani kuma ta tattara shawarwari da masarautar Kano da hakimai suka bayar wurin gyara wannan doka ta masarautar Kano.
Mallam Ibrahim Ado Kurawa marubuci ne a kan lamuran sarauatar Kano kuma na hannun daman Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi na biyu ya kwantanta wannan mataki da siyasa amma ba dan saboda jama’a ko ci gaba ko kuma dan kara martabar Kano. Yace majalisa tana da ayyuka da dama a gabanta, amma sai ta gagguata yin aiki a kan wannan batu da ba zai amfanar da jama’a ba.
A yau Talata ne ake sa ran kwamitin majalisar dokokin Kano dake gudanar da aikin garanbawul ga dokar kula da aikace-aikacen majalisar masarautar Kano zai mika rahotonsa ga zauren majalisa. Sababbin masarautun da ake sa ran majalisar dokokin Kano zata shigar cikin daftarin dokar sauarautar Kanon, sun hada da Gaya da Karaye da Bichi da kuma Rano
Ga karin bayani daga wakilin mu na Kanon, Mahmud Ibrahim Kwari:
Facebook Forum