'Yan majalisar dokokin Amurka sun ce har yanzu tilas ne majalisa ta dauki matakan kare matasa bakin haure daga maida su kasashensu na asali, duk da dan Karin lokacin da aka samu daga kotun kolin Amurka, wadda taki sauraron daukaka karar da gwamnatin Trump tayi tana kalubalantar hukumcin da karamar kotu ta yanke na ci gaba da aiwatar da tsarin da ya kare wadanda iyayensu bakin haure suka shigo da su Amurka suna kanana da ake kira “Dreamers.”
Saneta Susan Collins ‘yar jam’iyar Republican mai wakiltar jihar Maine ta ce, za a jira a ga abinda zai faru game da ja in ja da ake yi a kotu kan shawarar da shugaba Donald Trump ya yanke ta dakatar da tsarin gwamnatin Obama da ya bayar da izinin yin aiki da kuma karatu ga wadanda iyayensu suka shigo da su Amurka tun su na kanana, tsarin da ake kira DACA.
Babu shakka hukumcin da kotun ta yanke ya rage matsin lambar da ‘yan majalisar ke fuskanta na daukar mataki kafin cikar wa’adin ranar biyar ga watan Maris, inji Collins. Sai dai ta ce wannan bai kawar da barazanar da wadannan matasa da ake kira Dreamers ke fuskanta ta tasa keyarsu zuwa kasashen da iyayensu suka taho da su daga can.
Alkalai a jihohin California da New York sun yanke hukumcin haramta dakatar da tsarin DACA, wanda shugaba Trump yake barazanar kawo karshenshi ranar biyar ga watan Maris. Kawo yanzu, majalisa bata amince da zaunannen tsarin da zai tantance matsayin masu cin moriyar shirin na DACA, da sauran wadanda ke iya amfana da shirin ba.
Facebook Forum