Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon yace Majalisar Dinkin Duniya zata yi nazarin barazanar matakan tsaro a dukkan ofisoshinta. Majalisar zata dauki wannan matakin ne a saboda harin bam din da aka kai ofishinta dake Abuja babban birnin taraiyar Nigeria.
A jiya talata Mr Ban ya fadawa kwamitin sulhu na Majalisar cewa Majalisar Dinkin Duniya zata yi nazarin harin da aka kai da kuma yin nazarin irin wannan barazana a duk fadin duniya.
Yace a filli yake cewa ‘yan ta’ada suna kara auna ofisoshin Majalisar da ma’aikatanta wajen kai hare hare. Yace mutane goma sha daya daga cikin ashirin da uku da aka kashe a Abuja ma’aikatan Majalisar ne.
Fiye da mutane tamanin ne suka ji rauni, a lokacinda wani mai harin kunar bakin wake ya kutsa kofofin fita na Majalisar ya shiga harabar ya aikata wannan danyen aikin.
-