Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Tana Jimamin Mutuwar Kofi Annan


 Kofi Annan
Kofi Annan

Tsohon babban maga takardar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Kofi Annan ya mutu da safiyar yau Asabar, kuma ya mutu yana da shekaru 80 a duniya.

Iyalan Annan da gidauniyarsa ne suka sanar da labarin mutuwarsa a cikin wani sakon Twitter, inda suka ce ya mutu cikin kwanciyar hankali bayan wata 'yar rashin lafiya a yau Asabar.


Sanarwar Twitter ta kwantanta Annan da cewa dattijon duniya ne wanda ya himmantu wajen kishin ci gaban kasashen duniya, kuma ya sadaukar da rayuwarsa wurin neman zaman lafiyar duniya. A lokacin aikinsa na jagorancin MDD, ya yi aiki tukuru wajen tabbatar da zaman lafiya, da aiwatar da shirye shiryen ci gaba da kare hakkokin bil adama da bin tsarin doka da oda.


Ita ma Majalisar Dinkin Duniyar ta aike da wani sakon Twitter a yau, tana jimamin wannan rashin babban mutum, shugaba kuma mai hangen nesa, sakon na cewar kayi rayuwa mai kyau kuma abin koyi.

Kofi Annan haifaffen Ghana, shine bakar fatar Afrika na farko da ya fara zama a matsayin babban maga takardan MDD daga 1997 zuwa 2006.


Kuma shine babban sakataren majalisar na farko da rike mukamai dabam dabam a matsayin ma’aikacin majalisar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG