ABUJA, NIGERIA - To sai dai kwararru a fanin tsaro da masu ruwa da tsaki na ganin ba nan gizo ke saka ba.
Yunkurin gyara wannan dokar ta'addanci ta shekara 2013 ya biyo bayan nazarin rahoton da kwamitin shari'ar 'yancin dan adam da al'amuran shari'a suka yi ne kamar yadda shugaban kwamitin Opeyemi Bamidele daga jihar Ekiti ya gabatar a gaban majalisar dattawa.
A jawabinsa Bamidele ya ce kudurin dokar ya tanadi haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta'adda, saboda a dakile karuwar satar mutane da karban kudin fansa masu yawa da suka wuce kima.
Bamidele ya ce gyararren dokar zai gindaya ka'idoji da tsare-tsare da nufin hana kungiyoyin 'yan ta'adda safarar kudade ta hanyar bankuna da sauran hanyoyin sadarwa na kudi.
Amma masanin harkokin tsaro Dokta Yahuza Ahmed Getso yana ganin akwai abin dubawa a harkar tsaron kasar baki daya ne.
Shi kuwa mai nazarin al'amuran tsaro kuma shugaban kamfanin bikon sikiruti Dokta Kabir Adamu ya ce akwai abubuwan da suka fi batun haramta kudin fansa da ya kamata a duba.
A nashi bayanin, tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma Kanar mai murabus Dangiwa Umar yana ganin dole ne a bada kudin fansa idan za a saki wadanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda: