Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Amaechi ya yi Zargin Yana Cikin Mutanen da Jonathan ke Son Hallakawa


Gwamnan Rivers Rotimi Amaechi
Gwamnan Rivers Rotimi Amaechi

Gwamna Rotimi Amaechi na jihar Rivers ya ce yana cikin mutanen da shugaba Jonathan ke son ya hallaka

Kwana kwanan nan tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaba Jonathan wasika mai shafi goma sha takwas. Kodayake shugaba Jonathan ya mayarda da martani a wata wasika mai shafi bakwai ya bar abubuwa da dama da bai bada amsa ba. A cikin wasikar ta Obasanjo ya zargi shugaba Jonathan da horas da wasu asu kashe mutane wadanda zasu hallaka mutane dubu d shugaban ya shirya sunayensu

A karon farko tunda gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da shugaba Jonathan suka shiga takunsakar siyasa wadda ta kai ga gwamnan barin jam'iyyar PDP zuwa ta APC bangarorin biyu sun soma yin cacar baki.

Gwamnan ya fito bainar jama'a yana zargin sunasa ne na daya a jerin sunayen mutane dubun da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya ambata a waskiarsa cewa shugaba Jonathan na shirin hallakawa domin wata mnufar siyasa. Gwaman ya ce idan mutum nada Ubangiji to haka asirin makiyansa zasu dinga tonuwa. Ya ce idan lokaci ya yi zai yi bayani dalla-dalla tre da bada hujjoji.

Sai dai mai ba shugaba Jonathan shawara kan harkokin siyasa ya ce zargin Amaechi bashi da tushe blantana gaskiya. Ya ce wasikar da Olusegun ya rubutawa shugaban kasa bata da tushe kuma ba gaskiya ciki. Ya ce shugaban kasa ya mayarda martani kuma ya ce idan Obasanjo ya san Ubangijinsa sai ya kawo hujjojinsa domin tabbatar da abubuwan da ya rubuta a wasikar. Shugaban kasa ya umurni jami'an tsaro su binciki maganar kuma ya gayawa Human Rights su ma su yi bincike. Ya ce Amaechi mutum ne wanda za'a ce tamkar kusoshin kansa sun kunce, wato ya soma hauka ke nan.

Wani Bello Abubakar da kan yi nazari kan harkokin siyasa ya yi tsokaci. Ya ce zargin da Amaechi ya yi abu ne na siyasa wanda idan aka cigaba a hakan ba zai haifi da mai ido ba. Siyasar ma kanta za'a yita ne kawai amma mutane ba zasu ci gajiyarta ba domin shugabannin da yakamata su taimakawa jama'a domin su samu cigaba sun shiga wani halin da ba zai anfani kowa ba. Ya ce ita siyasa ba za'a hana zargi ba amma ba irin wannan ba.

Ga rahoton Lamido Abubakar.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG