'Yan Jam'iyyar Republican a Majalisar Dattawa na shirin sake wani yinkuri a wannan satin, game da aniyarsu ta sake dokar kiwon lafiya da tsohon Shugaba Barack Obama ya kafa.
A tsawon watan jiya, Majalisar Dattawan ta gwada wasu kudurorin dokar kiwon lafiya biyu, wajen neman wadda za ta iya maye ta yanzu da aka fi sani da Obamacare nan take da kuma wacce za ta maye ta sannu a hankali cikin tsawon shekaru biyu saboda 'yan Majalisar su samu lokacin yin cikakken nazarin yadda za a maye gurbin ta yanzun.
Dukkannin kudurorin dokar sun gamu da adawa daga 'yan Democrats da kuma wasu 'yan Repulican ta yadda babu kudurin da ya yi nisa a yinkurin maida shi doka.
Sanata John Thune, daya daga cikin 'yan Republican 52 a majalisar mai kujeru 100, ya fadi jiya Lahadi cewa Shugaban Masu Rinjaye Mitch McConnel zai bude babin kuri'ar cigaba da muhawara ka daya daga cikin kudurorin da kuma duk wata kwaskwarimar da ake bukata.
Facebook Forum