Daka duka alamu yawan korafe-korafen zai zama tarihi idan majalisar dattawa ta gama yiwa dokar zabeta 2010 kwaskwarima. Majalisar ta kuduri aniyar yin hakan domin a kawo karshen cecekuce kan zaben 2015. Idan aka gyara dokar wato za'a yi zabukan kasar duka rana daya sabanin abun da hukumar zabe ta shirya a jadawalin da ta fitar.
A shirin INEC a watan biyu na 2015 za'a yi zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya. Daga bisani kuma a yi na gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jihohi lamarin da jama'a suk ki amincewa da shi musamman jam'iyyun adawa.
Abu Ibrahim dan majalisar dattawa shi ya gabatar da kudurin a yiwa dokar zabe gyara ya kuma kara haske a kan lamarin. Yace kuduri na farko shi ne a gyara dokar zabe domin a yi zabuka duk rana daya. Yace a wasu kasashe haka a keyi domin babu wani dalili da zai sa a yi zaben shugaban kasa kuma sai bayan mako biyu kafin a yi sauran. Idan an bar dokar haka idan shugaban kasa ya ci zabe zai yi anfani da hukumar zaben da hukumomin tsaro ya yi abun da yake so. Na biyu kudin da INEC zata kashe nada yawa. Misali a zaben 2011 INEC ta kashe nera biliyan hamsin banda kudin ma'aikata da jami'an tsaro. A wannan shekarar INEC tace tana neman nera biliyan dari da biyu amma abun da aka bata biliyan arba'in da biyar. Wannan ya nuna kasar ba zata iya ba. A yi komi rana guda a gama
Ko domin rage kashe kudi da gujema wasu abubuwa yakamata a yi zabukan rana guda. Abu Ibrahim yace batun cewa mutanen karkara ba zasu gane ba ba gaskiya ba ne. Abun da yakamata a yi shi ne ayi kuri'u da launi daban daban. Misali ta zaben shugaban kasa ana iya bata jan launi.
Sanata Alkali Jajere daya daga cikin 'yan kwamitin dake kula da harkokin zabe yace za'a iya yin zabe rana guda a karkara. A daina ganin mutanen kauye kamar kawunansu basu waye ba. Idan sha'anin zabe ne babu abun da zai rudar dasu. Sun saba yin zabe.
Ga rahoton Medina Dauda.