ABUJA, NIGERIA - Hakan ya bayyanu a fili ne lokacin da majalisar dattawan ta ki amincewa da bukatar Shugaba Mohammadu Buhari na neman a gyara sabuwar dokar zabe ta shekara 2022, bayan an yi wa dokar karatu na biyu.
Abinda Majalisar dattawa ta yi dangane da kin amincewa da gyara sashi 84 karamin sashi ne 12 a sabuwar dokar zabe ta shekara 2022, wani abu ne mai kama da jurwaye da kamar wanka. Domin ta ce ba umurnin kotu ta bi ba, amma abin da ta yi daidai yake da bin umurnin kotun.
Sai dai shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan, Yahaya Abdullahi Abubakar, yana ganin yawan ‘ya’yan jamiyyar APC da su ka kai 70 a majalisa dattawan, na iya ba su karfin sauya ko wani irin mataki da ya tunkare su a majalisar, to sai dai a wannan karon, matakin da kotun tarayya Abuja ta dauka ne ya fusatar da su.
Shi kuwa, shugaban Kwamitin kula da harkokin hukumar zabe a majalisar dattawan sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce haka dimokradiya ta gada.
Amma kwararre a fanin shari'a kuma masanin kundin tsarin mulki Mainasara Kogo Ibrahim Umar, ya ce wannan mataki da majalisar dattawa ta dauka, juyin juya hali ne a dimokradiyar kasar.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai, majalisar wakilai ba ta ce komai ba akan batun gyaran kashi 84 karamin kashi na 12 ba, wanda ya ce duk wani mai mukamin gwamnati da yake sha'awar tsayawa takara a lokacin zabe, to ya ajiye aiki wattani shida kafin jam’iyyar sa ta tsayar da shi a matsayin dan takara.
Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda: