Majalisar ta yi kiran ne a zaman da ta yi a ranar Talata inda ta nemi a maye gurbin manyan jami'an tsaron kasar da masu sabbin dabaru kamar yadda kafofin yada labaran Najeriya suka ruwaito.
Kiran na zuwa ne bayan kisan gillar da aka yi wa wasu manoma 43 da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne a karamar hukumar Mafa a jihar Borno.
Wata sabuwar muhawara kuma da ta sake kunno kai ita ce ta neman a dauko dakarun haya, abin rahotanni suka ce gwamnan jihar Borno Prof. Babagana Umara Zullum ya goyi baya.
Daya daga cikin mambobin kwamitin dattawan na al’ummar arewa maso gabashin Najeriya Mallan Abba Kaka ya ce, abin takaici ne a ce a cikin shekaru 11 an kasa shawo kan matsalar tsaro.
Ya kara da cewa, ya kamata gwamnatin ta samar da sojan haya domin a ganinsa wannan kadai ita ce hanyar da za a kawo karshen ayyukan ta’addanci a kasar.
Wannan ba shi ne karon farko da 'yan majalisar dokokin Najeriya suke neman a sauke manyan hafsoshin ba, ko a watan Janairu majalisar dattawan ta yi makamancin wannan kira bayan da ta lura al'amuran tsaro na kara tabarbarewa a kasar.
Saurari Karin bayani cikin sauti a Rahoton Umar Farouk Musa: