Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ba Ta Amince Da Aika Sojoji Zuwa Kasar Nijar Ba


Taron Kaddamar Da Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya
Taron Kaddamar Da Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya ta ce ba za ta amince wa Shugaba Tinubu ya aika da sojoji zuwa  kasar Nijer ba, a bisa wasu muhimman dalilai da sai Majalisar ta yi zama na musamman akan su. 

A cikin wasikar da Shugaba Tinubu ya aika wa Majalisar ya nemi goyon bayan su kan matakin da Kungiyar ECOWAS ta dauka ciki har da tsoma baki kan maido da dimokradiyya a makwabciyar kasar.

Bayan karanta wasikar da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya yi a zauren Majalisar sai Sanata Abdul Ningi ya kawo kuduri na jan hankalin Majalisar a game da bukatar Tinubu

Ningi ya ce yaki ba abin wasa ba ne, kuma musamman yakin da ya hada da iyaka, a yankin Arewa kusan jihohi bakwai ne suka hada iyaka da kasar Nijar, abu ne mai wuya mutum ya banbanta 'yan asalin Nijar da 'yan Najeriya da ke kan iyaka, saboda haka dole ne Majalisa ta yi taka tsantsan. Ningi ya ce shugaban kasa bashi da hurumin daukar wannan mataki shi kadai ba tare da ya kawo dalilansa a gaban majalisa ba.

Shi kuwa gagarabadan Majalisar dattawa wanda shi ne tsohon shugaban Kwamitin kula da harkokin soji, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya yi tsokaci cewa dokar kasa ba ta ba Majalisa dama ta amince da wannan mataki ba, kuma doka ba ta ba shugaban kasa hurumin yin gaban kansa ba. Ndume ya ce da kaman kasar Nijer ce ta kawo wa Najeriya hari, to za a yarda Najeriya ta mayar da martani, amma a yanzu kam sanatoci na shiyyar Arewa ba za su amince da irin wannan yunkuri ba ko da an samu wani akasi. Ndume ya ce gara a bi ta hanyar diflomasiyya idan ana so a samu maslaha, kuma wannan shi ne abinda aka yarda da shi

Shi ma Sanata Rufa'i Sani Hanga ya ce akwai abin dubawa a yadda bukatar shugaban kasa ta taho Majalisar domin bai kamata a kawo masu shi kamar sanarwa ba, haka bai dace ba. Hanga ya ce sai an kawo bukatar, Majalisa ta rufe kofa ta tattauna akan bukatar tukuna saboda shiga yaki ba karamin abu ba ne. Hanga ya ce akasarin 'yan majalisar ba za su yarda da wannan bukata ba domin yakin zai shafi abubuwa da dama a kasar musamman ma rayukan al'umma.

Kungiyar ECOWAS wanda Tinubu ke shugabanta ta bai wa sojojin Nijar mako guda daga ranar Lahadi da ta gabata su maido da hambararren shugaban Kasar Mohammed Bazoum kan mukaminsa ko kuma su fuskanci tsauraran takunkumai.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG