Wannan mataki da Majalisar dattawan ta dauka ya biyo bayan wani kuduri ne da sanata Emmanuel Udende ya gabatar a zauren Majalisar jiya laraba inda ya koka cewa an kashe mutane sama da 50 a wasu sabbin hare haren da yan ta'adda suka kai a wasu kauyukan jihar Binuwai da suka hada da Kwande, Ukum, Logo, da Katsina Ala.
Majalisar ta bukaci shugabanin hukumomin tsaro da su gaggauta tura jami'an tsaro domin magance cigaba da hare haren da 'yan ta'adda masu dauke da makamai su ke kwaiwa a fadin kasar.
A bayanin sa, Sanata Adamu Aliero ya yi nazari cewa, Majalisar na da rahottani da shawarwari tun daga shekara 2015 inda ya ce kullum ana kawo masu rahoton kashe mutane ana tagayara su, ana kuma kona garuruwa, da hana mutane shiga gonakin su domin su yi noma saboda a samu abinci.
Aliero ya ce yanzu shugabanin Majalisar za su kai wadannan rahottanin ga Shugaban kasa kuma suna so a aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahottanin.
Shi kuwa sanata mai wakiltan Jigawa ta Arewa Maso Yamma, Babangida Husseini ya ce Majalisa tana aikin ta na sa ido kan ayyukan shugabanin hukumomin tsaron kasar kuma ba za su gajiya ba.
Babangida ya ce Majalisa ba ta taba yanke kudaden da ake bayarwa a kasafin kudi domin tsaro ba, kuma majalisa tana aikin sa ido kan aiyukan tsaron nan, saboda haka Majalisa za ta zauna da bangaren zantaswa domin gano inda matsalar ta ke.
A hirar shi da Muryar Amurka, kwararre a harkokin tsaro Dokta Yahuza Ahmed Getso ya ce ba a nan gizo ke saka ba. Ya kamata Majalisa su duba yanayin biyan albashin jami'an tsaro da farko kafin su duba yadda za a bada shawarwari kan shawo kan rashin tsaron.
Getso ya ce akwai alamun lauje cikin nadi domin tun ba yau ba Majalisa ke gayyatar shugabanin hukumomin tsaron nan, kuma suna cewa sun gamsu da bayanan da ake ba su. Getso ya ce wannan yunkuri ba zai yi wani tasiri ba sai in Majalisa ta yanke kudaden ta, ta tabbatar jami'an tsaro sun samu isassun kudade na albashi da na biyan bukatun su.
Abin jira a gani shi ne irin matakin da bangaren zantaswa zai dauka idan an mika rahottanin.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna