Mallam Garba Shehu ya tabbatar da hakan ne a ranar Asabar, amma ya ce cutar ba ta nakasa shi ba, a cewar gidan talabijin na Channels.
Ya bayyana cewa yana jin wasu 'yan alamun cutar, yanayin da ke da alaka da nau’in omicron na coroanavirus, ya kuma kara da cewa yanzu haka ya killace kansa, kuma zai ci gaba da karin wasu gwaje-gwaje.
Mai magana da yawun shugaban wanda ya kuma riga ya karbi cikakken allurar rigakafin cutar ya tabbatar da cewa babban sakatare a fadar shugaban kasa, Tijjani Umar da wasu ma’ikatan fadar Aso Rock suma an yi musu gwajin COVID-19.
Sai dai ya ce ba shi da masaniya kan sakamakon gwanjin nasu.
Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan da hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da samun karin mutane 4,035 da suka kamu da cutar, adadi mafi yawa na kwana guda da aka bayar tun bayan bullar cutar a kasar a watan Fabrairun 2020.
Yayin da hukumomi suka ayyana bullar cutar a karo na hudu, NCDC ta kuma tabbatar da sabbin kamuwa da cutar har 1,940 da 1,356 a ranakun Alhamis da Juma'a.
Ya zuwa karfe 7 na yammacin ranar Asabar, Najeriya ta tabbatar da adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai 234,709 sannan daga cikin adadin mutane 212,237 da suka kamu da cutar sun warke daga cutar yayin da wasu 2,993 suka mutu.