Hanna, mahaukaciyar guguwa ta farko a shekarar 2020, ta sauka a kudancin gabar tekun Texas da maraicen ranar Asabar 25 ga watan Yuli.
Haka kuma a ranar ta Asabar, kusan tazarar kilomita 6,000 yamma da yankin, aka fidda sanarwar gargadin yiwuwar aukuwar mahaukaciyar guguwa a tsibirin Oahu da ke Hawaii, inda ake sa ran guguwar wadda aka yi wa lakabi da Douglas za ta sauka yankin ranar Lahadi 26 ga watan Yuli.
Mahaukaciyar guguwar Hanna ta sauka gabar tekun yankin, kilomita 24 arewa da garin Port Mansfield da ke jihar Texas, tafe da isaka mai gudun kilomita 145 a cikin sa’a guda. Cibiyar sa ido kan mahaukaciyar guguwa ta Amurka ta ce ana sa ran guguwar za ta haddasa ambaliyar ruwa da iska mai karfin gaske.
Facebook Forum