Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahara Sun Kai Hari Kan Ma'aikatar Sarrafa Sinadarai Ta Arewacin Iraq


Wuta Da Hayaki Turnuke Da Sama Bayan Kai Harin Ma'aikatar Mai Ta Bai Hassan a Kirkuk, Iraki, July 31, 2016.
Wuta Da Hayaki Turnuke Da Sama Bayan Kai Harin Ma'aikatar Mai Ta Bai Hassan a Kirkuk, Iraki, July 31, 2016.

Jami’ai a Iraki sun ce mahara sun kai wasu hare-hare guda biyu akan wata ma’aikatar sarrafa sinadaran kimiyya a arewacin kasar, inda suka kashe akalla mutane 5 duk a yau Lahadi.

Abin ya faru ne a yankin da ke karkashin ikon Kurdawa a lardin Kirkuk. Jami’an suka ce harin farko ya faru ne a kimanin tazarar kilomita 15 daga arewa maso yammacin Kirkuk, daga baya kuma maharani suka banka wuta.

Hari na biyu kuma ya faru ne a kusa da ma’aikatar man fetur ta Bai Hassan, maharani sun yi damara da rigar bam suka hallaka wani injiniya daya da kuma jikkata wasu mutane guda 5.

Akalla an kashe mahara guda 3 daga cikin 4 da suka kai harin. To amma har yanzu ba wani tabbacin ko maharani sun tayar da damarar bam din da ke jikinsu ne ko kuwa sun yi harbi ne har suka kashe mutanen.

XS
SM
MD
LG